Hebrews 11

Ta Wurin Bangaskiya

1Bangaskiya ita ce kasance tabbacin abin da muke bege a kai da kuma tabbatar da abin da ba mu gani ba. 2Abin da aka yabi kakanni na dā a kai ke nan.

3Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani. 4Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadayar da ta fi wadda Kayinu ya miƙa. Ta wurin bangaskiya aka yabe shi cewa shi mai adalci ne, saʼad da Allah ya yi magana mai kyau game da bayarwarsa. Ta wurin bangaskiya kuma har yanzu yana magana, ko da yake ya riga ya mutu.

5Ta wurin bangaskiya ne aka ɗauki Enok daga wannan rayuwa, ta haka bai ɗanɗana mutuwa ba; ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi. Gama kafin a ɗauke shi, an yabe shi a kan ya gamshi Allah. 6In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yǎ gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.

7Ta wurin bangaskiya Nuhu, saʼad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya.

8Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim, saʼad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasar da zai karɓi gādo daga baya, ya kuwa yi biyayya ya tafi, ko da yake bai san inda za shi ba. 9Ta wurin bangaskiya ya yi zama a ƙasar da aka yi masa alkawari kamar baƙo a baƙuwar ƙasa; ya zauna a tentuna, haka ma Ishaku da Yaƙub, waɗanda su ma magādan alkawarin nan ne tare da shi. 10Gama yana zuba ido ga birnin nan mai tushe, wanda mai zānen gininsa da kuma mai gininsa Allah ne.

11Ta wurin bangaskiya Ibrahim, ko da yake shekarunsa sun wuce-Saratu kanta kuma bakararriya ce-ya iya zama mahaifi domin ya
Ko kuwa Ta wurin bangaskiya Saratu ma, wadda shekarunta sun wuce, ta iya haifi ʼyaʼya domin ta
amince cewa shi wanda ya yi alkawarin mai aminci ne.
12Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, zuriya masu yawa suka fito kamar taurari a sararin sama da kuma kamar yashin da ba a iya ƙirgawa a bakin teku.

13Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya saʼad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya. 14Mutane masu faɗin irin abubuwan nan sun nuna cewa suna neman ƙasar da take tasu. 15Da a ce suna tunanin ƙasar da suka bari a baya, da sun riga sun sami damar komawa. 16A maimako, suna marmarin wata ƙasa mafi kyau-ta sama. Saboda haka Allah ba ya kunya a kira shi Allahnsu, domin ya riga ya shirya musu birni.

17Ta wurin bangaskiya Ibrahim, saʼad da Allah ya gwada shi, sai ya miƙa Ishaku hadaya. Shi da ya karɓi alkawaran ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa, 18ko da yake Allah ya ce masa, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”
Far 21.12
19Ibrahim ya yi tunani cewa Allah yana iya ta da matattu, a misalce kuwa, ya sāke karɓan Ishaku daga matattu.

20Ta wurin bangaskiya ne Ishaku ya albarkaci Yaƙub da Isuwa game da nan gabansu.

21Ta wurin bangaskiya ne Yaƙub, saʼad da yake bakin mutuwa, ya albarkaci kowane ɗan Yusuf, ya kuma yi sujada yayinda yake jingine a kan sandansa.

22Ta wurin bangaskiya ne Yusuf, saʼad da kwanakinsa suka yi kusan ƙarewa, ya yi magana game da fitowar Israʼilawa daga Masar ya kuma ba da umarni game da ƙasusuwansa.

23Ta wurin bangaskiya ne iyayen Musa suka ɓoye shi har wata uku bayan haihuwarsa, domin sun ga cewa shi ba kamar sauran yara ba ne, ba su kuwa ji tsoron umarnin sarki ba.

24Ta wurin bangaskiya ne Musa, saʼad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Firʼauna. 25Ya zaɓa yǎ sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yǎ ji daɗin shaʼawace-shaʼawacen zunubi na ɗan lokaci. 26Ya ɗauki wulaƙanci domin Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya zuba ido ga ladansa. 27Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba; ya kuwa jure domin ya ga wannan wanda ba a iya gani. 28Ta wurin bangaskiya ya kiyaye Bikin Ƙetarewa ya kuma yayyafa jini, domin kada mai hallakar ʼyaʼyan fari yǎ taɓa ʼyaʼyan fari na Israʼila.

29Ta wurin bangaskiya ne mutane suka bi ta cikin Jan Teku, sai ka ce a kan busasshiyar ƙasa; amma da Masarawa suka yi ƙoƙari su yi haka, sai aka nutsar da su.

30Ta wurin bangaskiya ne katangar Yeriko ta rushe, bayan mutane suka yi ta kewaye ta har kwana bakwai.

31Ta wurin bangaskiya ne ba a kashe Rahab karuwan nan, ta tare da marasa biyayya ba don ta marabci ʼyan leƙan asiri.

32Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Samaʼila, da kuma annabawa, 33waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki, 34suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe. 35Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau saʼad da aka ta da matattu. 36Waɗansu suka sha baʼa da bulala. Waɗansu kuwa suka sha ɗauri da sarƙa aka kuma jefa su cikin kurkuku. 37Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci—  38duniya ba ta ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka.

39Waɗannan duka an yabe su saboda bangaskiyarsu, duk da haka babu waninsu da ya sami abin da aka yi alkawari. 40Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga makasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu.

Copyright information for HauSRK